An kashe mutane 133 a Gaza a cigaba da rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa

76

Wani jakadan Amurka ya isa Tel Aviv, babban birnin Isra’ila, don tattauna batun sasanta rikici, yayin da ake cigaba da gwabza fada tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Jakadan, Hady Amr zai shiga tattaunawar da Isra’ila, Falasdinawa da jami’an Majalisar Dinkin Duniya da fatan za su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Da sanyin safiyar yau, Isra’ila ta kai hare-hare ta sama a Gaza kuma mayakan Falasdinawa sun mayar da martani ta hanyar harba rokoki zuwa Isra’ila.

Fadan da aka yi cikin kwanaki 5 da suka gabata na daga cikin rikice-rikice mafiya muni da aka yi a yankin cikin shekaru.

Rikicin ya fara ne a ranar Litinin kuma ya biyo bayan rikita rikita ta tsawon makonni Isra’ila da Falasdinu a Gabashin Kudus.

Karuwar tashin hankali ya kai ga rikice-rikice a masallachi mai tsarki wanda Musulmi da Yahudawa ke girmamawa.

Akalla mutane 133 aka kashe a Gaza sannan 8 sun mutu a Isra’ila tun fara yakin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − five =