Aman wutar dutse ya kashe mutane 15 a Congo

48

Mazauna yankin Goma a Gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na komawa gida bayan wani aman wutar dutse da ya faru a birnin.

Mutane 15 ne suka mutu akasarinsu a yayin da suke kokarin tserewa.

An harbi mutum hudu yayin da suke kokarin guduwa daga wani gidan yari a yankin na Goma.

Dubban jama’a sun tsere cikin firgici bayan da tsaunin Nyiragongo ya rufta. Lamarin ya janyo barna ga gidaje.

Wata kungiya da aikinta shi ne yin hasashen yiwuwar fuskantar aman wutar dutse ta ce aikinta ya fuskanci koma-baya saboda rashin kudi.

Hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tace ana fargabar batan yara sama da 170 tare da raba wasu 150 da iyayensu, inda ta kara da cewa za a kafa cibiyoyi domin taimakawa yara kanana.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − 10 =