Shugaba Buhari ya dawo daga London

22

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan kammala ganin likitansa a London.

Jirgin saman shugaban kasa, wanda ya dauko shugaban kasar daga London, ya sauka a filin jiragen saman kasa da kasa na Nmandi Azikiwe dake Abuja, a yau da yamma.

Shugaban Kasar ya bar kasarnan a ranar 30 ga watan Maris da ya gabata, domin a duba lafiyarsa a karon farko cikin sama da shekara guda.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana adawa da tafiyar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce tace tafiyar ta nuna gazawar gwamnatinsa.

Masu zanga-zanga sun mamaye gidan ofishin jakadancin Najeriya dake London, a lokacin ziyarar shugaban kasar zuwa Birtaniya.

Shugaba Buhari ya samu tarba daga ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello, da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da sauran hadiman shugaban kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 1 =