Rundunar Yansandan Taraba ta fara neman wadanda suka kashe jami’anta

50

Rundunar yansandan jihar Taraba ta aika da wata tawagarta domin kama wadanda ke da hannu a kisan wasu yansanda biyu.

Kakakin rundunar, David Misal, ya gayawa manema labarai cewa tuni tawagar ta isa Takum bisa umarnin kwamishinan yansandan jihar, domin kama wadanda ke da hannu a kisan na Takum da kuma kara tsaro akan dukkan titunan dake yankin.

Ana samun yawaitar hare-hare ‘yan bindiga akan titunan yankin cikin yan makonninan.

An gano cewa yan bindiga ne suka yiwa yansandan biyu kwanton bauna aka kashe su a wani wajen duba ababen hawa akan titin Takum zuwa Katsina-Ala.

Hakan ya kawo adadin yansandan da yan bindiga suka kashe tare da sace makamansu a yankin cikin yan makonninnan zuwa 4.

Karin bincike ya kuma bankado cewa akalla mutane 17 ne yan bindiga suka kashe akan titin Wukari zuwa Takum da Takum zuwa Kashinbila da titin Takum zuwa Katsina-Ala, cikin makonnin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 2 =