Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji biyu na kasa da kasa sun yi kira da a aike da agajin gaggawa zuwa yankin Sahel na Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Sun ce mutane miliyan 29 da ke yankunan na bukatar taimako, ciki har da yara miliyan 1 da dubu 600 da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Hare-haren daga masu ikirarin jihadi ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira rashin tsaro mara misaltuwa tare da raba mutane miliyan 5 da rabi da muhallansu.
Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi kuma yawaitar yunwa ya haura zuwa matakin mafi girma a cikin kimanin shekaru goma.
Kasashe shida da abin ya shafa sune Mali da Nijar da Burkina Faso da Chadi da wasu sassan Najeriya da Kamaru.
A wani labarin kuma, fursunoni sama da 30 sun tsere bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan motar ‘yansanda da ke jigilarsu zuwa kotun shari’a a kasar Afirka ta Kudu.
Kakakin ‘yansanda na KwaZulu Natal, Brigadier Jay Naicker, ya ce ‘yansanda na neman wadanda suka tsere.