Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shirin rage talauci na kasa

51

Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da wani shirin rage fatara da samar da cigaba wanda kwamitin ba wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki ya samar.

Mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman akan kafafen yada labarai da huldar jama’a, Femi Adesina, ya sanar da haka a yau ga manema labaran fadar shugaban kasa a Abuja.

A cewar Femi Adesina, kwamitin gudanarwar shirin rage fatarar zai samu shugabancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda zai bayar da ka’i’dojin aiwatar da shirin gabadaya.

Yace majalisar ta kuma amince da aiwatar da shirin tare da shigar da shi cikin kundin cigaban kasa mai matsakaicin wa’adi na shekarar 2021 zuwa 2025 da kuma manufofin cigaba na shekarar 2050. Majalisar ta kuma umarci Attoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’ah, Abubakar Malami, da ya shirya wani kudirin da za a aikawa majalisar kasa domin samun dorewar aiwatar da shirin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × five =