Majalisar dattawa ta amincewa Buhari ya ciyo bashin sama da N1trn

28

Majalisar Dattawa ta amincewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ciyo bashin kasashen waje na Dala Biliyan 1 da Miliyan 500 da Euro Miliyan 995, kwatankwacin jumillar sama da naira tiriliyan 1.

Amincewar ta biyo bayan aiki da rahoton kwamitin majalisar dattawa na basukan cikin kasa da kasashen waje, wanda shugaban kwamitin Clifford Odia, ya gabatar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a watan Mayun bara, ya aika da wasika zuwa majalisar dattawa yana neman amincewarta domin sake ciyo wasu basuka daga waje domin bai wa gwamnatinsa damar samar da kudaden cike gibin kasafin kudin 2020 da ayyuka masu muhimmanci tare da agazawa wasu jihoshin kasarnan.

Gwamnatin tarayya tace za ayi amfani da basukan wajen aiwatar da ayyukan da aka fi bukata tare da tallafawa gwamnatocin jihoshi farfado da tattalin arzikinsu, wanda annobar corona ta daidaita.

Da yake gabatar da rahoton, Clifford Ordia, yayi nuni da cewa yawanci basukan basu da kudin ruwa mai yawa, kuma akwai isasshen lokacin biya.

Masana sun bayyana damuwa dangane da karuwar yawan basukan da ake bin Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + 4 =