Majalisar Dattawa a yau ta tabbatar da nadin Dr. Halilu Shaba a matsayin darakta janar na hukumar binciken sararin samaniya ta kasa.
Majalisar ta dattawa ta bayar da tabbacin nadin ne biyo bayan duba rahoton kwamitin majalisar dattawa na kimiyya da fasaha, yayin zamansa a Abuja, karkashin jagorancin Sanata Uche Ekwunife.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 2 ga watan Maris na bana, ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Halilu Shaba a matsayin darakta janar na hukumar binciken sararin samaniya.
A wasikar, Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan majalisa da su dubi bukatarsa wajen gaggauta amincewa.
Halilu Shaba ya kasance a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar biyo bayan karewar wa’adi biyu na Farfesa Saidu Mohammed a watan Yunin 2020.
Hukumar tunda farko a ranar 2 ga watan Yunin 2019, ta sanar da nadin Jonathan Angulu a matsayin mukaddashin darakta janar.