Kungiyar Tarayyar Afrika ta yi kiran a kawo karshen mulkin soja a Chadi

96

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi kira da a kawo karshen mulkin soja a kasar Chadi, wacce ‘yan tawaye suka kashe shugaban kasar.

Sojoji sun gaggauta sanar da cewa dan Idriss Déby zai shugabanci majalisar soja har tsawon watanni 18 kafin a gudanar da zabe.

Kasar wacce a baya ke karkashin mulkin mallakar Faransace, wacce ke da babban sansanin soja a Chadi, ta nuna goyon baya ga karbe mulkin don samun kwanciyar hankali.

Jam’iyyun adawa ma sun yi Allah wadai da abin da suka kira juyin mulki na gado.

Kungiyar kwadago ta yi kira da a gudanar da yajin aikin gama gari, yayin da kungiyar ‘yan tawayen ta ce kasar ta Chadi ba masarauta ba ce.

Kwamitin wanzar da zaman lafiya da tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka ya nuna damuwa game da juyin mulkin na sojoji wadanda suka nada Janar Mahamat Déby Itno mai shekaru 37 a kan karagar mulki tare da soke majalisar kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + fourteen =