JNI ta yi watsi takardar da ke alakanta Pantami da mutuwar Yakowa

80

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana takardar da ke alakanta Ministan Sadarwa Isa Pantami da shirin kisan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Patrick Yakowa da cewa ta bogi ce.

Kungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su binciki makarkashiyar da ake zargi da kuma asalin takardar.

Takardar wacce ta fara bayyana a internet a shekarar 2010, ta yi zargin cewa a taron da aka yi a watan Yulin 2010 da Kungiyar ta shirya kuma Pantami ya jagoranta, akwai wasu makirce-makirce da aka kulla da suka hada kashe Yakowa.

Sakatare-janar na kungiyar, Khalid Aliyu, ya fada a cikin wata sanarwa a jiya cewa zargin yana da ban tsoro kuma abin kyama ne, sannan yana mamakin yadda za a rubuta makircin kisan kai a takarda kuma a ajiye.

Aliyu ya ce Pantami bai taba rike shugabancin Kungiyar ba, a matakin kasa ko jiha.

Ya kara da cewa kafafen yada labarai ne suka yada wannan takarda don ingiza yan Najeriya wajen tarwatsa zaman lafiyar kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + 4 =