Jam’iyyar APC ta amince da gazawa wajen kula da tsaro

67

Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa yanayin tsaro a fadin kasarnan abin damuwa ne, inda ta bayyana halin da ake ciki da kalubalen gwamnatinnan.

Jam’iyyar ta kuma ce gwamnatinta, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tana samun nasarori da dama wajen samar da ababen more rayuwa a fadin kasarnan.

Jam’iyyar ta APC, a wata sanarwa da sakatarenta na riko na kasa, John Akpanudoedehe ya fitar, tace baza ta siyasantar da halin tsaro a kasarnan ba.

Halin tsaro a kasarnan ya kara tabarbarewa a makon da ya gabata inda aka kashe jumillar mutane 200 da sace wasu 44 a fadin Najeriya, kamar yadda wani bincike ya nuna.

A sanarwar, jam’iyyar ta APC tace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na aiki tukuru wajen ganowa da hukunta masu tayar da zaune tsaye.

Jam’iyyar ta nemi a hada kai, inda tace akwai bukatar hakan wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukkan ‘yan Najeriya ke bukata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − two =