Kungiyar malaman makarantun polytechnics (ASUP) sun tafi yajin aiki.
Shugaban kungiyar na kasa, Anderson Ezeibe, ya sanar da haka a wani taron manema labarai a Abuja yau da safe.
Ya ce ‘ya’yan kungiyar sun amince su kulle dukkanin polytechnics na kasarnan har sai an biya musu bukatunsu.
Hakan na zuwa bayan yunkurin gwamnatin tarayya na magance tafiya yajin aikin a makarantun.
An rawaito cewa ministan ilimi, Adamu Adamu, a jiya da yamma, ya gayyaci kungiyar domin wani zaman ganawa na gaggawa, biyo bayan barazanar tafiya wani yajin aikin.
Amma shugaban kungiyar, a wajen taron manema labaran, yace an fara aiki da hukuncin ‘ya’yan kungiyar na rufe dukkanin makarantun na polytechnics a fadin kasarnan, farawa daga yau.