An kashe 3 daga cikin daliban Jami’ar Greenfield da aka sace a Kaduna

43

Ma’aikatar tsaro ta jihar Kaduna ta ce yan bindiga sun kashe dalibai uku na na Jami’ar Greenfield da aka sace a Jihar.

Cikin wani sakon Twitter da ma’aikatar ta fitar ta ruwaito Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i ya yi Allah-wadai da wannan mummunan rashin imani na salwantar da rayuwar dan adam.

Ya kara da cewa dole a yaki wadannan ‘yan bindiga ta ko wanne hali.

Ya kuma aika da ta’aziyyarsa ga mutanen jihar da iyayen yaran da suka rasa yarukansu.

Ya kuma ce gwamnati za ta cigaba da shaidawa mutanen jihar halin da ake ciki game da lamarin.

Har yanzu dalibai 29 daga cikin 39 da aka sace a kwalejin aikin gona ta Afaka dake Kaduna, suna hannun yan bindiga.

An sace su a watan Maris, amma 10 daga cikinsu sun tsira bayan iyayensu sun tattauna da yan bindigar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 7 =