Yan bindiga sun sace sama da mutane 60 a Zamfara

159

Yan bindiga sun sace mutane sama da 50 a wani hari a kauyen Tungar Baushe dake gundumar Mutunji a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

An tabbatar da cewa an kone gidaje a hare-haren wadanda aka kaddamar a jiya da dare.

Tunda farko yan bindigar sun nemi mazauna Tungar Baushe da su biya harajin da suka kayyade musu domin kauracewa hari.

Amma mazauna garin suka gwammace su gudu zuwa wani kauyen dake makotaka da ake kira Ruwan Tofa.

Matakin nasu ya tunzura yan fashin dajin, wadanda suka bazama zuwa Ruwan Tofa kuma suka zakulo wadanda suka arce daga Tungar Baushe.

Yan bindigar sun kone rumbuna da gidajen mutane a Ruwan Tofa.

An kasa samun kakakin yansanda na jihar, SP Muhammad Shehu, domin tofa albarkacin baki, har kawo lokacin hada wannan rahoton.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − two =