Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya

30

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya, kasancewar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tafiya zuwa London a kasar Ingila domin a duba lafiyarsa.

Zaman ganawar majalisar ya samu halarta a zahirance daga shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da babban mai bayar da shawara kan tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da wasu ministoci 7.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, da sauran mambobin majalisar, sun shiga ganawar ta internet.

Kafin fara ganawar, an yi shiru na minti daya domin karrama tsaffin ministoci 2 da suka rasu, da tsohon ministan kimiyya da fasaha, Sanata Bode Olowoporoku da Alhaji Umaru Muhammad Baba.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda ya sanar da mutuwar tasu, yayi bayani kan mukamai daban-daban da suka rike da ayyuka daban-daban da suka yiwa kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen − ten =