‘Ya’yan kungiyar ma’aikatan majalisa ta kasa a jihar Jigawa sun kulle kofar shiga majalisar dokokin jihar Jigawa, kasancewar sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga yau.
Sun tafi yajin aikin ne bisa gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da yancin cin gashin kai na kudade ga bangaren majalisa.
Shugaban kungiyar na jihar, Umar Kazaure, yace yajin aikin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da kungiyar ta bawa gwamnati ta aiwatar da yancin cin gashin kai na kudade ga bangaren majalisa.
Umar Kazaure yace kungiyar ta yi hakuri tsawon shekaru 2 bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan dokar yancin cin gashin kai amma gwamnonin jihoshi suka kasa aiwatar da ita.
Yace kungiyar za ta cigaba da yajin aikin har sai an biya musu bukatunsu.
Umar Kazaure ya kuma ce muddin gwamnonin jihoshi suka gaza biya musu bukatunsu, kungiyar zata tsunduma yajin aiki a fadin kasarnan.
A wani lamarin irin wannan, kungiyar ma’aikatan majalisa ta kasa, reshen majalisar dokokin jihar Yobe, ta rufe kofar shiga majalisar dokoki bisa yancin cin gashin kai na kudade ga bangaren majalisa.
Shugaban kungiyar na jihar, Comrade Zanna Ali, wanda ya jagoranci zanga-zangar, yace baza su kyale yan majalisar dokokin jihar su halarci zaman majalisar na yau ba, har sai an biya musu bukatunsu.
Yace zanga-zangar bin umarni ne daga uwar kungiyar ta kasa.
A cewarsa, an dauki matakin hakan ne sanadiyyar kasa aiwatar da yancin cin gashin kai na kudade ga bangaren majalisa da na shari’ah, wanda zai tabbatar da cikakken yanci ga bangarorin gwamnatin biyu.
A wata sanarwa, shugaban kungiyar na kasa, Comrade Usman Ahmed, yace kungiyar ta gama bin dukkan hanyoyin da ya kamata ta bi wajen ganin an aiwatar da dokar.