Gwamnatin Kaduna ta roki kotu ta yankewa Zakzaky hukunci

53

Babban lauya mai gabatar da kara a shari’ar da ake yiwa shugaban kungiyar yan’uwa musulmi ta Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, da matarsa, Zeenat, ya nemi babbar kotun Kaduna ta soke gabatar da kariya daga wadanda ake tuhuma kuma ta yanke musu hukunci kamar yadda shari’ah ta tanada.

Babban lauyan, Dari Bayero, lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan mai shari’ah Gideon Kurada, ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Mayu domin wadanda ake tuhuma su gabatar da kariya a shari’ar, yace gwamnatin jihar ta kammala gabatar da kara bayan ta gabatar da mai bayar da shaida na 15 a shari’ar.

Amma lauyan Sheikh Zakzaky, Femi Falana, ya gayawa manema labarai cewa tawagarsa zata fara gabatar da kariya a shari’ar a ranar da za dawo zama.

Femi Falana, wanda ya samu wakilcin Marshall Abubakar, ya ce bayan sun duba takardun wadanda ake kara, za a shiga bayar da kariya kan tuhume-tuhumen da ake musu.

A cewarsa, tun a baya masu kariya sun roki kotun da ta yi watsi da shari’ar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 − 1 =