Dubban mutane sun rasa muhallansu bayan gobara a sansanin ‘yan Rohingya

35

Ana fargabar cewa yawan wadanda suka mutu a gobarar da ta kama a sansanin yan gudun hijira na Rohingya, suna karuwa, yayin da gomman dubban mutane suka rasa gidajensu bayan gobarar.

Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 7.

Kungiyar dake kula da yan gudun hijira ta jiyo wasu da suka shaida lamarin na cewa wayar da ta katange sansanonin na Cox’s Bazar a kasar Bangladesh ta hana mutane dayawa tsiri, ciki har da yara.

Sansanin wani bangare ne na jerin sansanonin dake dauke da sama da yan gudun hijira miliyan 1, wadanda suka arce daga Myanmar tun daga shekarar 2017.

Kungiyoyin agajin yan gudun hijira sun yi kiyasin cewa tsakanin mutane dubu 40 da 500 zuwa dubu 50 ne gobarar ta shafa.

Dayawa suna samun mafaka a sansanonin dake makotaka ko matsugunan abokai ko na yan’uwa, da makarantu, a cewar shirin abinci na majalisar dinkin duniya, wanda ya kuma ce wuta ta kone wasu daga cikin cibiyoyinsa na abinci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × five =