Buhari ya nada Isa Dutse a matsayin daraktan zartarwa a hukumar Bankin Raya Musulunchi

31

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mahmoud Isa-Dutse a matsayin Daraktan Zartarwa a Hukumar Bankin Raya Addinin Musulunci a Jedda, Saudi Arabia.

Isa Dutse shi ne tsohon Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa. Ya yi hulda da abokan hulda na cigaba da cibiyoyin hada-hadar kudade na duniya yayin zamansa na Babban Sakatare. Ya saba da tsarin aikin manyan hukumomi kamar Bankin Raya Musulunci kuma ana matukar girmama shi a hukumomin.

Kafin nada shi a matsayin Babban Sakatare, Isa Dutse ya kasance Shugaban riko kuma daga baya ya zama Daraktan da ba na-zartarwa ba na Asusun bunkasa ababen more rayuwa na Afirka. Ya kasance mashahurin ma’aikacin banki ne wanda ya kwashe shekaru 23 yana da kwarewa a fannin hada-hadar kudade, bayan ya kammala karatunsa a fannin Tsimi da Tattalin Arziki tare da MBA da kuma Ph.D a fannin kula da kasuwanci.

Isa Dutse ya karbi mukamin ne daga hannu Shuaibu Gambo wanda aka nada a ranar 1 ga watan Yulin, 2011 kuma ya rike mukamin na tsawon kimanin shekaru 10.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 4 =