An samu karuwar tsadar kayan masarufi da kayan abinci a Najeriya

56

Hukumar kididdiga ta kasa a yau tace an samu karuwar tsadar kayan masarufi da kashi 17.33 cikin 100 a watan Fabrairun da ya gabata.

Wannan shine tashin farashi mafi yawa da aka samu cikin shekaru 4.

A watan Janairu, tsadar kayan masarufin ya hau da kashi 16.47 cikin 100, daidai lokacin da ake fuskantar tashin gwauron zabi da farashin kayan abinci suka yi.

Hukumar tace tsadar kayan abinci ya karu zuwa kashi 21.79 cikin 100 a watan Fabrairu, idan aka kwatanta da kashi 20.57 cikin 100 da aka samu a watan Janairun bana.

Hukumar tace hakan shine mataki mafi muni da aka kai tun bayan da aka fara tattara alkaluman a jere, cikin sama da shekaru 10.

Farashin kayan abinci ya hau a makonnin da suka wuce, bayan an sanar da hana kai kayan abinci da shanu daga Arewa zuwa Kudu.

Matakin ya haifar da tashin farashin naman shanu da kayan abinci da kayan gwari, musamman a jihoshin kudu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 − six =