Rahotanni daga Libya sun ce an gano gawarwaki kusan 15, hannayensu daure su da ankwa, kuma jefar da su a garin Benghazi da ke gabashin kasar.
Jami’an tsaro sun killace yankin da ke kusa da masana’antar siminti yayin da suke gudanar da bincike a wajen.
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin gida sun yi tir da Allah wadai bisa kisan gillar da kungiyoyi masu dauke da makamai suke yi a Benghazi da kewaye.
Dakarun da ke biyayya ga Khalifa Haftar, kwamandan sojoji dake da iko da gabashin Libya.
A watan Nuwamban da ya gabata, an harbe Hanan al-Barassi, fitacciyar mai fafutuka da ke sukar Janar Haftar, a kan wani titi mai cike da hada-hada a Benghazi.