An kwantar da mutane 56 bisa wata bakuwar cuta a Kano

16

Akalla mutane 56 mazauna garin Gwangwan da ke jihar Kano rahotanni ke cewa suna fama da amai da fitsarin jini, sakamakon barkewar wata bakuwar cuta da ta addabi garin.

Gwangwan, wanda ke da nisan kilomita 136 daga birnin Kano, yana cikin Karamar Hukumar Rogo, ya fada cikin yanayin mai ban tsoro, inda mutane ke zaman fargaba da rudani.

Wani mazaunin garin, Muhammad Tukur, ya ce lamarin ya shafa wurare shida a kauyen, kuma kimanin mutane 56 sun kamu da cutar tun barkewarta.

Wani magidanci, wanda yaransa biyu suka kamu, ya yi korafin cewa ya zuwa yanzu ya kashe sama da naira dubu ashirin a asibiti yana kokarin ganin an kula da su duk da mawuyacin halin da suke fuskanta na rashin kudi.

Wani da abin ya shafa, wanda a gidansa mutum takwas suka kamu, ya ce yana cikin damuwa matuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 16 =