An kaddamar da fara allurar rigakafin corona yau a abuja

62

An kaddamar da rigakafin corona yau a Najeriya, bayan an yiwa wani likita, Dr Cyprian Nyong, na babban asibitin kasa dake Abuja, rigakafin.

Shugaban kwamitin corona na shugaban kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya kaddamar da aikin rigakafin, a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wajen kaddamarwar, sakataren zartarwa na hukumar lafiya matakin farko ta kasa, Dr Faisal Shu’aib, ya bayyana lamarin a matsayin tarihi.

A ranar Talata aka kawo alluran rigakafin guda miliyan 4 zuwa Najeriya, ta filin jiragen saman kasa da kasa na Nmandi Azikwe dake Abuja.

A gobe Asabar, za a yiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo, rigakafin domin kawar da kokonto a zukatan yan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + 15 =