Akalla ma’aikata 16 ne suka mutu a wata gobara da ta tashi a jiya a wata masana’antar kayan cinna wuta a kudancin kasar Indiya.
Kimanin wasu ma’aikata 32 ne suka jikkata a lamarin a wani kauye da ke jihar Tamil Nadu.
Jami’in ‘yansanda na yankin Raj Narayanan ya ce yayin da yawancin wadanda abin ya shafa suka kone kurmus a wurin, wasu kuma sun mutu a asibiti.
Adadin wadanda suka mutu na iya karuwa kamar yadda aka ce da dama daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
‘Yan sanda sun ce masana’antar tana aiki da lasisin da ya dace amma sun ce suna kokarin gano musabbabin afkuwar gobarar da kuma bincikar ko kamfanin na amfani da abubuwan fashewa da kayan da aka yarda da su.
Fira-Ministan Indiya, Narendra Modi, yayi ta’aziyya ga rayukan da suka salwanta a wannan lamari duk da kasancewar hukumomin kasar sun sanar da biyan diyya ga iyalan wadanda suka mutu.