Yan kwandago sun soki Sylva saboda yace a saurari ukuba bisa karin farashin danyen mai

111

Kungiyar kwadago ta TUC ta soki karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, wanda ya gayawa yan Najeriya cewa su shirya shan ukuba mai alaka da karin farashin danyen mai.

Kazalika, kungiyar masu masana’antu ta Najeriya da kungiyar ciniki da masana’antu ta Lagos da sauran masu ruwa da tsaki, sun shawarci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da karin farashin danyen man a kasuwannin duniya wajen dakile fatara da talauci tare da samar da cigaban ta kowane bangare.

Kungiyoyin sun sanar da haka yayin wata ganawa daban-daban a jiya tare da manema labarai, lokacin da suke mayar da martani akan kalaman na Timipre Sylva, wanda ya gargadi yan Najeriya da su saurari cin moriya da kuma ukubar da zata biyo bayan hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Najeriya wacce ta dogara da danyen mai domin kusan kashi 50 cikin 100 na kudaden shigar gwamnati, da kuma sama da kashi 90 cikin 100 na kudaden da ake samu daga kasashen waje, karuwar farashin danyen man na nufin karuwar kudaden shiga ga kasar.

A daya hannun, karuwar farashin danyen man yana kuma nufin karuwar farashin albarkatun man, kasancewa kasar ta dogara kacokan akan shigo da tataccen mai sanadiyyar rashin tace man a cikin kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 2 =