Tsananin sanyi ya kashe mutane 21 tare da raba miliyoyi da wutar lantarki a Amurka

46

Tsananin sanyi da zubar dusar kankara sun yi sanadin mutuwar akalla mutum 21 a Amurka, sannan miliyoyin mutane sun rasa wutar lantarki.

Babu wutar lantarki a Texas inda bukatar wutar da ake da ita tayi wa tashar lantarkin yawa.

Miliyoyin mutane a jihar, wadanda ba su cika shiga yanayin tsananin sanyi irin haka na suna ta fafutukar yadda za su zauna babu wutar lantarki a wannan yanayin.

An yi hasashen cewa tsananin sanyin zai cigaba har zuwa karshen mako.

Mace-macen da aka samu saboda munin yanayin sun faru ne a jihohin Texas da Louisiana da Kentucky da North Carolina da kuma Missouri.

Hukumar Yanayi ta Amurka tace fiye da Amurkawa miliyan 150 ne ke cikin shirin ko ta kwana dangane da yanayin.

Sannan hukumar ta ce a jiya Talata dusar kankara ta lullube fiye da kashi 73 cikin 100 na Amurka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − six =