Shugaba Sassou Nguesso na neman wa’adi na hudu a kasar Congo-Brazzaville

41

Mahukunta a Congo-Brazzaville sun gabatar da sunayen mutane takwas masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar ga kotun tsarin mulki don tabbatar da su gabanin zaben ranar 21 ga watan Maris.

Shugaba Denis Sassou Nguesso zai kara da abokan adawa su bakwai da suka hada da tsohon Ministan Kudi Mathias Dzon da dan wani tsohon firaminista.

Sassou Nguesso, mai shekaru 77, na neman wa’adi na hudu. Ya hau kan karagar mulki tun daga shekarar 1979, in ban da wasu shekaru biyar baya, ya fadi zabe a shekarar 1992.

Babbar jam’iyyar adawa ta ce za ta kauracewa zaben.

An canza kundin tsarin mulki a zaben raba gardama a shekarar 2015 inda aka cire yawan wa’adin mulki da shekarun yan takara. Nasarar da Sassou Nguesso ya yi a zaben shekarar 2016 ta haifar da tashin hankali da zargin magudin zabe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × five =