Shekaru 45 da kisan Janar Murtala Mohammed

134

A yau tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Murtala Ramat Muhammed, yake cika shekara 45 daidai da rasuwa.

An kashe tsohon shugaban kasar ne a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976 a birnin Legas.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yakin basasar da aka yi a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ya nemi balle yankin Biafra daga kasarnan.

A wannan lakacin janar Murtala ya jagoranci rundunar sojin da suka murkushe sojojin Biafra tare da kawo karshen yaki basasar baki daya kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.

Yana matsayin birgediya ne sojojin da suka yi juyin mulki na uku a Najeriya suka nada Janar Murtala a matsayin shugaban kasa, inda a watan Janairun shekarar 1976 aka kara masa girma zuwa janar.

Yana cikin shugabannin kasar da aka yi dake da kima sosai a idon yan kasarnan.

Duk rana ita yau ta 13 ga watan Fabrairu, ana tunawa da rayuwar Janar Murtala wanda ya fara tunanin dawo da Babban Birnin Tarayya daga Legas zuwa Abuja.

An haifi Mutarala Muhammed a ranar 8 ga watan Nuwambar 1938 a Kano, cikin zuriyar Fulani dake mulki. Mahaifinsa, Muhammed Riskuwa, ya fito daga zuri’ar Genawa, wadanda suke da tarihin ilimin shari’ar musulunchi, kasancewar kakansa da mahaifin kakansa, dukkansu sun ruke mukamin alkalin alkalan Kano.

Murtala Mohammed ya fara karatu a makarantar firamaren gidan sarki. Daga nan ya koma makarantar firamaren gidan Makama a Kano, wacce take daga wajen fadar sarki. Daga nan ya cigaba zuwa makarantar Middle ta Kano wacce ake kira Rumfa College a yanzu, a shekarar 1949, kafin daga bisani ya halarci shararriyar kwalejin gwamnati wacce yanzu ake kira da Barewa College Zaria, inda ya kammala karatunsa a shekarar 1957.

Ya nemi shiga aikin sojan Najeriya daga baya a shekarar 1957. Murtala Muhammed ya zama sojan Najeriya a shekarar 1958.

Allah SWT ya gafarta masa kura-kuransa, ya sanya shi a Aljanna. Ameen.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 − two =