Sabon shugaban sojoji na kasa Mozambique, Eugénio Ussene Mussa, ya mutu jiya bayan ya sha fama da cutar corona.
Ya mutu yayin da yake jinya a babbar cibiyar kiwon lafiya ta Mozambique, babban asibitin Maputo.
Kasa da wata guda kenan da hawan sa mulki, bayan an rantsar da shi a matsayin hafsan hafsoshin soji a ranar 20 ga Janairu.
Kafin hawa wannan mukami, ya kasance mai kula da wani aikin soji na musamman, wanda aikin sa shi ne yakar masu da’awar jihadi a lardin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas.
Ya fadawa faretin sojoji a watan da ya gabata cewa shekarar 2021 za ta zama shekarar yanke hukunci kan yaki da ta’addanci.
Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mozambique, Mirko Manzoni, ya aike da sakon ta’aziyya ga Shugaban Kasa Filipe Nyusi da kuma mutanen kasar.