Majalisa ta sanya kwamitocin da za su tantance sabbin manyan hafsoshin soji

24

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a yau ya mika bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na tabbatar da sabbin manyan hafsoshin soji, zuwa ga kwamitocin hadin gwiwa na sojin sama da sojin ruwa, domin tantance su.

Shugaban majalisar Dattawan, ya bawa kwamitocin wa’adin makonni biyu su gudanar da ayyukansu tare da gabatar da rahoto ga majalisar.

Kazalika, Sanata Ahmad Lawan a yau, ya umarci kwamitin harkokin kasashen waje da ya binciki tsofaffin manyan hafsoshin soji da Shugaba Buhari ya nada a matsayin jakadun kasarnan.

An bukaci kwamitin da ya kammala ayyukansa kuma ya gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.

A wani labarin makamancin wannan, Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamiti na wucin gadi don tantance sabbin manyan hafsoshin soji da aka nada.

Kwamitin mai mambobi 20, karkashin jagorancin shugaban kwamitin harkokin tsaro na majalisar, Babajimi Benson, an kaddamar da shi ne a yau bayan karbar wasika daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 12 =