Jami’an tsaro na Amotekun sun kama wata tirela makare da Fulani Makiyaya 80

167

Wasu jami’an Hukumar Tsaro ta Amotekun sun tare wata babbar mota dauke da mutane akalla 80 da ake zargin Fulani makiyaya ne a yankin titin Iwo da ke Ibadan, babban birnin Jihar ta Oyo.

Mutanen da aka dauko a cikin babbar mota rahotanni sun nuna cewa jami’an Amotekun ne suka tsayar da su kuma binciken gaggawa yasa an gano wasu kwari da baka da kibiyoyi da adduna a cikin motar.

Baya ga wannan, majiyoyi sun fadawa manema labarai cewa akwai babura kusan 25 a cikin motar wacce kuma ke dauke da shanu.

A lokacin da aka bincike, an bayar da rahoton cewa mutanen sun fadawa jami’an Amotekun cewa suna kan hanyarsu ne ta zuwa jihoshin Legas da Ogun.

An ce binciken ya ja hankalin mazauna yankin da suka yi dandazo zuwa wajen motar, amma don kauce wa rikici, an ce jami’an tsaron sun jagoranci motar da mutanen da ke ciki zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Unguwar Gwada a kan titin na Iwo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × two =