Gwamnatin Tarayya na shirin sayarwa ko jinginar da kadarorinta akalla 36 domin samun kudade, musamman wadanda za ayi amfani da su a kasafin kudin bana.
Kadarorin sun hada da na bangaren makamashi da masana’antu da sadarwa da kuma gine-gine.
Ana tsammanin fara sayar da su ko jinginar da su tsakanin watan Janairun da ya gabata zuwa watan Nuwamban badi.
Hakan na kunshe ne cikin wani daftari da jaridar Premium Times ta samu.
Daftarin wanda bangaren zartarwa ya aikawa majalisar kasa ya nuna sunayen kadarorin, da yadda za a sayar da su, da kuma lokacin da za a dauka ana cinikin, tare da farashinsu.
Manya daga cikin kadarorin sune hukumar kare muhallin Abuja da dakin taro na kasa da kasa dake Abuja (ICC), da wasu matatun man fetur da ba a ambaci sunayensu ba, da kamfanin aikawa da wutar lantarki (TCN), da hukumar fina-finai ta kasa, da sauransu.