Gwamnatin tarayya da ta jihar Neja sun fara tattaunawa da ‘yan fashin da suka sace dalibai a Kagara

107

Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja sun fara tattaunawa da ‘yan bindigan da suka sace daliban makarantar Kagara.

Wata majiya dake da masaniya kan lamarin na cewa gwamnatocin na tattaunawar ce ta hannun masu shiga tsakani bayan sace daliban a daren Talata.

Wasu shugabannin Fulani da kuma tubabbun ‘yan fashi ne ke jagorantar kokarin ceto yaran.

Majiyar ta kara da cewa an nemi wasu manyan tubabbun ‘yan fashin daji daga Zamfara da Katsina domin jagorantar tattaunawar.

Gwamnatin Jihar Neja ta ce mutane 42 ne aka sace ciki har da dalibai 27 da ma’aikata uku da iyalansu guda 12. Makarantar na da dalibai kusan dubu 1.

‘Yan bindigar sun kashe dalibi daya yayin da yake kokarin guduwa, inda suka harbe shi da bindiga har sau uku.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − twelve =