Gwamnatin Somaliya tace yan bindiga sun kai hari wajen tsayawar sojoji kusa da fadar shugaban kasa

27

Gwamnatin Somaliya tace yan bindiga sun kai hari wajen da sojoji ke tsayawa a babban birnin kasar, Mogadishu, kusa da fadar shugaban kasa.

A wata gajeriyar sanarwa, ministan tsaron kasar yace an tarwatsa harin.

Mazauna wajen sun bayar da rahoton jin karar harbe-harben bindigogi.

Hakan yazo awanni kadan kafin shirin jam’iyyun adawa a Somaliya na gudanar da zanga-zangar adawa da shugaban kasa Mohamed Abdullahi Farmajo bisa cigaba da mulki.

Wa’adinsa ya kare a makon da ya gabata, ba tare da zaben magajinsa ba, lamarin da ya jefa Somalia cikin rikicin siyasa.

Ana sa ran Shugaba Farmanjo zai gana da shugabannin larduna 5 na Somaliya, a kokarin kawo karshen kika-kikar ta siyasa.

A wani labarin kuma, an rawaito jin karar harbe-harben bindigogi a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, bayan kungiyar jagororin yan adawa sun take umarnin gwamnati na hana taruwar jama’a, suka gudanar da zanga-zanga.

Jami’an tsaro sun rufe dayawa daga cikin titunan birnin saboda zanga-zangar da aka yi shirin gudanarwa.

Jam’iyyun siyasa na neman shugaban kasa Mohamed Abdullahi Farmajo ya sauka daga mulki bayan wa’adinsa ya kare a makon da ya gabata, ba tare da zaben magaji ba.

BBC ta bayar da rahoton cewa anji karar harbe-harben bindigogin a sassa daban-daban na birnin.

Dan takarar shugaban kasa na bangaren adawa, Abdirahman Abdishaku, na daga cikin wadanda suka yi yunkurin jagorantar zanga-zangar.

Jami’an tsaro sun harbi iska domin tarwatsa wasu masu zanga-zangar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 6 =