Gwamnatin jihar Kwara ta amince da amfani da hijabi a duk makarantun gwamnati da ke jihar sannan ta umarci makarantu 10 da ta rufe a makon da ya gabata da su koma aiki a ranar Litinin.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kwara, Mamma Jibril, ya fitar a yammacin jiya.
Gwamnatin jihar, a ranar Juma’ar da ta gabata, ta bayar da umarnin rufe wasu makarantun sakandare 10 a Ilorin, babban birnin jihar, har sai an shawo kan takaddama kan amfani da hijabi.
A tarurrukan da aka yi da gwamnati, shugabannin al’ummomin Kirista da Musulmi sun ki janye matsayarsu.
Yayin da shugabannin musulmin suka dage cewa ya kamata a bar dalibansu su yi amfani da hijabi kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada, amma takwarorinsu na Kirista sun bukaci yin la’akari asalin addinin makarantun.