Gwamnatin Jigawa zata kai yanmata kasashen waje su yi karatun likita

85

Gwamnatin jihar Jigawa zata dauki nauyin karatun karin wasu yanmata zuwa kasashen waje domin yin karatun aikin likita.

Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jiha Dr Salisu Muazu ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.

Yace daga yau Juma’a zuwa ranar Alhamis 18 ga wata za a karbi takardun yanmatan da suke da sha’awar tafiya karatun a ofishin kwamishinan lafiya na jiha dake Dutse.

Dr Muazu ya bayyana cewa sai yan asalin jihar Jigawa ne kadai ake bukatar su gabatar da takardunsu.

Ya kara da cewa dole yanmatan su kasance yan kasa da shekaru 23 a duniya, kuma su tabbatar sun kammala karatun sikandare tare da samun credit biyar a turanci da lissafi da sauran darussan kimiyya guda uku.

A ranar Asabar 20 ga wata ne za a gudanar da jarabawar zabar wadanda suka cancanta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × five =