Gwamnatin Somaliya ta dakatar da taruwar jama’a bisa hujjar karuwar masu kamuwa da Corona.
Akwai yiwuwar matakin zai shafi zanga-zangar da aka shirya yi a gobe ta adawa da rashin tabbas a siyasar kasar bayan wa’adin Shugaban Kasa Abdullahi Farmanjo ya kare kafin a gudanar da zabe.
Majalisar ministoci ta zauna a jiya kuma ministan lafiya yayi jawabi dangane da halin da ake cikin kan cutar corona a kasar.
Ma’aikatar lafiya ta samu adadi mafi yawa na wadanda suka harbu da cutar da wadanda ta kashe a wannan watan.
Ministocin sun bayar da umarnin cewa dukkan ma’aikatan da ba na tilas ba, suyi aiki daga gida domin rage yaduwar cutar.
Kamar yadda yazo a sabon umarnin, an kuma rage tafiye-tafiye tsakanin larduna da bulaguron da ba na dole ba.
An samu mutane dubu 5 da 500 da aka tabbatar sun kamu da cutar corona a Somalia, ciki har da mutane 172 da suka mutu.