Fadar Shugaban kasa ta zargi ‘yan Najeriya dangane da rahoton Transparency International

30

Fadar Shugaban kasa a yau ta zargi ’yan Najeriya dangane da mummunar matakin da kasar ta samu a rahoton da kungiyar nan mai yaki da cin hanci da rashawa ta duniya, Transparency International, na shekarar 2020 kan cin hanci da rashawa inda Najeriya ta samu maki 25 daga 100 kuma ta kasance kasa ta biyu a cikin kasashen da suka fi cin hanci a Afirka ta Yamma, kazalika  ta kasance kasa ta 149 daga cikin kasashe 180 a cin hanci da rashawa.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da huldar jama’a, Malam Garba Shehu, ya sanar da haka a yau lokacin da ya bayyana cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels, kusan kwanaki biyu bayan da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya karyata rahoton na Transparency International.

Da yake amsa tambaya, Garba Shehu ya ce rahoton ya nuna cin hanci da rashawa ne na ‘yan Najeriya ba na gwamnatin Buhari ba.

Matsayin na Garba Shehu, ya banbanta da na Transparency International wanda ya tattara bayanai daga bangarori 13 da suka hada bayanan masana da masu gudanar da kasuwanci kan wasu halaye na rashawa a bangaren gwamnati da suka hada da cin hanci, da karkatar da kudaden jama’a, da amfani da ofishin gwamnati don azurta kai da son zuciya a aikin gwamnati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + nine =