Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kamawa tare da hukunta da dukkan masu dauke da mamakai ta haramtacciyar hanya a kasarnan, ba tare da la’akari da kabilarsu ba.
Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya sanar da haka a jiya a wani shirin gidan talabijin na Channels.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi cewa yawaitar masu mallakar makamai yana kara rura wutar rashin tsaro a fadin kasarnan.
Femi Adesina yace shugaban kasar baya ragawa dukkan masu tayar da zaune tsaye kuma bazai saurarawa duk wanda hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo ba.
Yace shugaban kasar a koda yaushe yana kan bakansa na cewa a cafke tare da gurfanar da dukkan wanda aka kama dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba, ko daga ina ya fito.
Dangane da batun yunkurin fadar shugaban kasa wajen kawo karshen rikicin makiyaya, Femi Adesina yace an cimma wasu matsayoyi domin magance matsalar.