Buhari ya aika da jami’an tsaro zuwa Neja dangane da sace daliban Kagara

40

Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da huldar jama’a, Garba Shehu. Yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci dakarun soji da yansanda su tabbatar da gaggauta dawo da dukkan daliban da aka sace a kwalejin kimiyya ta gwamnati dake Kagara a yankin karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Yace shugaban kasar ya kuma aika da wata tawaga zuwa Minna, babban birnin jihar, domin tsara yadda za a ceto daliban da kuma ganawa da jami’an gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki.

Garba Shehu ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

Ya kara da cewa shugaban kasa ya tabbatar da dukkan goyon bayan gwamnatinsa ga dakarun soji a yakin da suke da mayaka da mahara, inda ya hore su da suyi duk mai yiwuwa wajen kauracewa aukuwar irin wannan harin a makarantu nan gaba.

Garba Shehu ya labarto shugaban kasar na cewa yana addu’a ga iyalan wadanda aka sace.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 7 =