Bazoum Mohamed ya lashe zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar

42

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar ta ce Bazoum Mohamed na jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki ne ya lashe zagaye na biyu na zaben da aka gudanar ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI ta fitar dazunnan sun nuna cewa Bazoum ya samu kuri’a miliyan 2 da dubu 501 da ‘yan kai.

Dan takarar jam’iyyar RDR, Mahamane Ousmane, wanda yake biye masa, ya samu kuri’a sama da miliyan 1 da dubu 968.

BBC ta rawaito cewa hukumar zaben ta CENI ta sanar da sakamakon dukkan gundumomi 266 na kasar.

A ranar Lahadi aka gudanar da zaben zagaye na biyu inda aka fafata tsakanin Mohammed Bazoum da abokin karawarsa Mahamane Ousmane.

Bazoum dai ya samu goyon bayan ‘yan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko na zaben, shi kuma Ousmane ya samu goyon baya daga gamayyar jam’iyyun hamayya guda 18.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 3 =