An samu adadi mafi karancin tun watan Disamba na wadanda ke kamuwa da corona a kowace rana a Najeriya

50

Najeriya ta samu raguwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a rana guda tun farkon zagayowar cutar a karo na biyu a watan Disambar da ya gabata.

An sake samun sabbin masu kamuwa da cutar su 685 a jiya a jihoshi 16, wanda ke nuna matukar raguwa daga mutane 1,883 da aka bayar rahoton sun kamu a shekaranjiya.

Adadin na baya-bayan nan ya kara jumillar yawan wadanda suka harbu da cutar a kasar zuwa 131,242, Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar da hakan a daren jiya.

Har ila yau, Najeriya ta samu mutuwar mutane takwas sanadiyyar corona a jiya, wanda ya kawo yawan adadin wadanda cutar ta kashe zuwa 1,586.

Tun farkon watan Disamba, an samu karuwa masu harbuwa da mace-mace sanadiyyar corona a fadin kasar.

Daga cikin wadanda suka kamu da cutar su 131,242, mutane 104,989 sun warke a fadin kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − 14 =