Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin Kano da yansanda kara a gaban kotu

63

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano da ‘yansanda da ke jihar zuwa kotu don a bi masa hakkin sa.

Malamin ya garzaya wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kano jiya, yana neman umarnin da zai hana gwamnatin jihar da ‘yan sanda cigaba da rufe masallacinsa da kuma hana shi yin wa’azi.

Wadanda ake kara a karar sun hada da Gwamnatin Kano da Babban Lauyan jihar da Kwamishinan ‘yan sanda.

A halin yanzu, kotun karkashin jagorancin mai shari’a Lewis Allagoa, ta dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu tare da bayar da umarnin a gabatar da sammaci ga wadanda ake kara kafin ranar da za a sake sauraron karar.

A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Kano ta hana malamin yin wa’azi kan abin da ta bayyana da yanayin wa’azinsa da ke rura wutar rikici.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =