Yansandan Najeriya sun sake kama Sowore

24

Hukumar Yansandan Najeriya ta sake kama mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, saboda jagorantar zanga-zanga a babban birnin tarayya, Abuja.

An kama Sowore tare da wasu yan gwagwarmaya yayin zanga-zangar, wacce aka shirya da nufin gudanarwa a fadin kasarnan, a jajibirin sabuwar shekara.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar wadanda suka tsira daga kamen, sun tabbatarwa da manema labarai cewa an yi awon gaba da Sowore a daya daga cikin manyan motocin yansandan Najeriya, wadanda aka tura zuwa wajen da ake gudanar da zanga-zangar a mahadar Gudu dake Abuja.

Duk da kasancewar majiyarmu bata san inda aka kai Sowore ba bayan anyi kamen, an gano cewa an kai tsohon dan takarar shugaban kasar zuwa ofishin yansanda na Abbatuwa ake Logokoma a Abuja, inda aka kulle shi tare da sauran.

Kakakin yansanda, Frank Mba, bai amsa kiran wayarsa ba, domin tofa albarkacin baki dangane da labarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + 19 =