Wadanda suka mutu a harin da aka kai jihar Yammacin Darfur a Sudan sun kai 83

44

Adadin mutanen da suka mutu a harin da yan bindiga suka kai a El Geneina, babban birnin jihar Darfur ta Yammacin Sudan, ya kai 83, kuma wadanda suka ji rauni sun kai 160, a daidai lokacin da mahukuntan Sudan suka yanke shawarar tura jami’an tsaro zuwa yankin.

A cewar wata sanarwa daga Majalisar Kolin Sudan, Kwamitin Tsaro na Sudan a jiya ya yanke shawarar tura karin jami’an tsaro zuwa Darfur ta Yamma don kare yyan kasar da muhimman abubuwan amfani.

Sanarwar ta lura cewa majalisar, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Kolin, Abdel Fattah Al-Burhan, ta gudanar da taron gaggawa a jiya don tattauna rikice-rikicen da suka faru a El Geneina a ranar Asabar.

Ta kara da cewa majalisar, wacce dake da wakilanta daga majalissar dokoki da majalisar zartarwa da hukumomin tsaro, sun kuma yanke shawarar kafa wani babban kwamiti da zai binciko abubuwan da suka faru a El Geneina, don tantance tushen matsalar da kuma gabatar da shawarwari game da shi, da dawo da doka da oda don hukunta wadanda suka aikata aika-aikar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − four =