Shugaba Buhari yayi ganawar sirri tare da Shugaba Patrice Talon na Benin

18

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da takwaransa na kasar Jamhuriyar Benin, Patrice Talon, a fadar Shugaban Kasa dake birnin Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa shugaban na Benin, wanda ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 11 da mintuna 9 na safe, ya samu tarba da shugaba Buhari.

Babu dai cikakken bayani ko karin haske kan batutuwan da shugabannin biyu suka tattaunawa a kai.

Sai dai akwai rahotannin da ke cewa Talon na ganawa da Buhari ne domin gode ma sa kan sake bude iyakokin Najeriya a watan Disamban 2020.

Ana kuma dai sa ran shugabannin biyu su kuma tattauna kan batun da suka shafi tsaro da sauran matsalolin da suka dangancin kasashen biyu da sauran yankunan kudu da hadamar saharar afrika

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × one =