Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman masu hali da suyi adalci wajen sukar gwamnatinsa.
A cewar wata sanarwa da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya fitar, Shugaban yayi kiran ne yayin da ya karbi bakuncin sakataren zartarwa na Hukumar Alhazai ta Kiristocin Najeriya, Rabaran Yakubu Pam, a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.
Yace duba da wadatar da ake da ita, gwamnatinsa ta samu nasarori da dama a fannoni daban-daban.
Buhari ya kuma ba gwamnatinsa maki kan yanayin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Kodayake ya yarda cewa har yanzu akwai abin da ya kira matsalolin Boko Haram da ake samu lokaci zuwa lokaci, Shugaban yace an samu ci gaba sosai idan aka kwatanta da rayuwar mazauna jihohin da abin ya shafa a baya.
Buhari ya kuma tabbatarwa da ‘yan gudun hijira cewa jin dadin su shine kan gaba a manufofi gwamnatin sa.