Masu hakar ma’adanai 22 ne suka makale a karkashin kasa kimanin kwanaki 2 bayan wata fashewa a wani wajen hakar ma’adanai a gabashin kasar China.
Fashewar ta auku a wani wajen hakar ma’adanai dake wani gari a kusa da birnin Qixia a lardin gabashi na Shandong.
Wata sanarwa da aka saki a ranar Litinin da dare tace fashewar ta lalata matattakalar fitowa daga wajen hakar ma’adanan da kuma na’urar sadarwa, a saboda haka hukumomi baza su iya ganawa da masu hakar ma’adanan ba.
Amma hukumomin sun aika da masu ceto zuwa wajen hakar ma’adanan.
Ana yawaitar samun hadari a wajen hakar ma’adanai a kasar China, inda masana’antar ke da dokokin kariya masu rauni.
A watan Disambar da ya gabata, masu hakar ma’adanai 23 ne suka makale a wani wajen hakar ma’adanai a birnin kudu maso yamma na Chongqing, watanni kalilan da mutuwar wasu mutane 16 sanadiyyar shakar guba bayan sun makale a karkashin kasa a wani wajen hakar ma’adanai dake birnin.