Matasan Fulani makiyaya sun yi wata yarinya fyade a Bauchi

66

Wasu matasan makiyaya Fulani su uku da aka kama a Bauchi bisa zargin aikata fyade ga wata yarinya da aka boye sunanta a karamar hukumar Itas/Gadau da ke jihar sun ce sun aikata laifin ne saboda suna son su gwada abin da suke kallo a bidiyon batsa.

Wadanda ake zargin sun yi magana daya bayan daya a wata hira da manema labarai yayin da aka gabatar da su a helkwatar rundunar ‘yansanda dake Bauchi a jiya sun ba da labarin laifin da suka aikata.

Babban wanda ake zargi, Mamman Jauro, dan shekara 15, mafi yawan shekaru a cikinsu, yace sun ga wanda suka yi wa fyaden ne kawai a daji kuma suka hada baki a tsakaninsu suka yi aika-aikar.

An ruwaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, reshen jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya fada wa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu, 2021, kamar yadda aka kai rahoto zuwa helkwatar yansanda ta garin Itas.

Ya ce an kama mutanen uku ne bayan wani rahoto da matar da iyayenta suka shigar saboda ta shaida wadanda ake zargin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 10 =