Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta kara shekarun barin aikin malaman makaranta

14

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da Dokar Gyaran Aikin Malaman Makaranta ta 2021.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya sanar da hakan a jiya yayin da yake yi wa ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa bayanin abin da ya faru a yayin taron majalisar karo na 30 ta bidiyo da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Adamu ya ce kudirin da aka amince da shi wanda ke neman ba da goyon baya na doka ga sabbin matakai da gwamnati mai ci yanzu za ta bi don inganta aikin koyarwa a kasar za a tura shi ga Majalisun Kasa don dubawa da yiwuwar amincewa.

Idan ‘yan majalisar tarayya suka amince da kudirin, shekarun ritayar malaman za su koma daga shekaru 60 zuwa 65 yayin da shekarun aiki kuma za su koma daga 35 zuwa 40.

Ya ce wasu daga cikin abubuwan da kudurin ya kunsa sun hada da bullo da kyautar kudi da alawus na musamman ga wadanda aka tura karkara da sauran matakai don jawo hankalin masu basira zuwa koyarwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 1 =